Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da wanda ya zo wurin zaman mutane da ya yi musu sallama, idan kuma ya yi nufin ya tashi daga wurin to ya yi wa mutanen wurin bankwana da yin sallama; dan sallamar farkon lokacin zuwa ba ta fi mafi cancanta daga ɗayar sallamar a lokacin da zai bar wurinba.
Fa’idoji
Kwaɗaitarwa akan yaɗa sallama.
Kwaɗaitarwa akan yin sallama ga mutanen dake zaune a lokacin haɗuwa da kuma lokacin juyawa.
Sindi ya ce: Faɗinsa: (Idan ya yi nufin tashi) wato: Daga majalisar. (To ta farkon bata kasance mafi cancanta ba) wato: Su biyun gaba ɗayansu sunnah ne da yin aiki da su, dan haka babu wata fuska ga barin ta biyu tare da tabbatar data farkon.
Madogara
سنن أبي داود (7/ 500) (5208).
سنن الترمذي (4/ 432) (2706).
السنن الكبرى للنسائي (9/ 144) (10129).
مسند أحمد (12/ 47) (7142).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (11/ 360).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 142).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص523).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 672).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com