Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Da wani mutum zai maka leken asiri ba da izinika ba, sai ka jefe shi da dutse, har ka cire masa ido: ba laifi yin hakan

عن أبي هُريرة -رضي اللهُ عنه- مرفوعًا: «لو أن رجلا -أو قال: امْرَأً- اطَّلَعَ عليك بغير إِذْنِكَ؛ فَحَذَفْتَهُ بحَصَاةٍ، فَفَقَأْتَ عينه: ما كان عليك جُنَاحٌ».
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Da wani mutum zai maka leken asiri ba da izinika ba, sai ka jefe shi da dutse, har ka cire masa ido: ba laifi yin hakan
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya bada labari cewa da wani zai leka gidan wani ta bayan kofa ko ta saman katanga ko makamanci hakan, sai ya jefe shi da dutse ko ya soke shi da wani karfe a ido, to ba wani abu na zunubi ko na kisasi; Don kuwa shi ya janyowa kansa.

Madogara

1- صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. 2- صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. 3- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. 4- تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار علماء السلف، الطبعة: الثانية 1414هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ƘISASI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com