Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَوَّلُ مَا يُقْضَى بَيْنَ النَّاسِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِي الدِّمَاءِ».
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa farkon abinda za’a yi hukunci a tsakanin mutane a zalincin junansu a ranar Alkiyama: A jinane ne, kamar kisa da raunuka.

Fa’idoji
  1. Girman al'amarin jinane, domin farawa tana kasancewa ne da abu mafi muhimmanci.
  2. Zunubai suna girmama ne da gwargwadan barnar da take afkuwa da su, salwantar da rayuka kubutattu yana daga mafi girman barna babu mafi girma daga gare shi sai kafirci da yi wa Allah - Madaukakin sarki - shirka.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 2) (6864). صحيح مسلم (3/ 1304) (1678). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص319). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص640). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 103).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR LAHIRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com