Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «رَغِمَ أَنْفُ، ثُمَّ رَغِمَ أَنْفُ، ثُمَّ رَغِمَ أَنْفُ»، قِيلَ: مَنْ؟ يَا رَسُولَ اللهِ قَالَ: «مَنْ أَدْرَكَ أَبَوَيْهِ عِنْدَ الْكِبَرِ، أَحَدَهُمَا أَوْ كِلَيْهِمَا فَلَمْ يَدْخُلِ الْجَنَّةَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ƙasƙanci da taɓewa har saida hakan ya kai, kai ka ce ya ɗora hancinsa a cikin ƙasa - ya maimaitata sau uku - sai aka tambaye shi: Waye wannan ya manzon Allah wanda ka yi mummunar Addu’a akansa? Sai (Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata aagre shi - ya ce: Wanda ya riski mahaifansa a lokacin tsufa - ɗayansu ko su biyun -, ba su zama sababi na shigarsa aljanna ba; hakan saboda rashin kyautata musu da kuma saɓa musu.

Fa’idoji
  1. Wajabcin biyayya ga mahaifa, kuma hakan yana daga sabubban shiga aljanna, musamman ma a lokacin tsufansu da rauninsu.
  2. Saɓawa iyaye yana daga manyan zunubai.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 1978) (2551). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 394). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (1/ 308). فيض القدير شرح الجامع الصغير، زين الدين المناوي (4/ 34). شرح النووي على مسلم، (16/ 108).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN BIN IYAYE

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com

Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba · Hadisai tare da sharhi · Sabīl