Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan ɗayanku ya ji wani abu a cikinsa, sai ya rikitar da shi cewa shin wani abu ya fita daga gare shi ko a'a, to, kada ya fita daga masallaci har sai ya ji kara ko ya ji waji wari

عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا وَجَدَ أَحَدُكُمْ فِي بَطْنِهِ شَيْئًا، فَأَشْكَلَ عَلَيْهِ أَخَرَجَ مِنْهُ شَيْءٌ أَمْ لَا، فَلَا يَخْرُجَنَّ مِنَ الْمَسْجِدِ حَتَّى يَسْمَعَ صَوْتًا، أَوْ يَجِدَ رِيحًا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya ji wani abu a cikinsa, sai ya rikitar da shi cewa shin wani abu ya fita daga gare shi ko a'a, to, kada ya fita daga masallaci har sai ya ji kara ko ya ji waji wari".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -yana bayyana cewa idan wani abu ya yi kai-kawo a cikin cikin mai sallah, sai ya rikitar da shi; shin wani abu ya fita daga gareshi ko a'a? to, kada ya fita daga sallarsa ya yanketa don sake alwala, har sai ya tabbatar da samun karin da ya ɓata alwalarsa; ta hanyar ya ji karar tusa, ko ya ji wari; domin abin aka tabbatarw to kokwanto ba ya ɓata shi, shi tabbas ya tabbatar da tsarki (alwala) kari kuma akwai kokwantone a cikinsa.

Fa’idoji
  1. Wannan Hadisin asali ne daga asalin Musulunci, kuma ƙa'ida ne daga ƙa'idojin fiƙihu, ita ce: lallai Yakini ba ya gushewa da kokwanto, asali shi ne wanzuwa a kan abin da ake a kansa, har sai an tabbatar da saɓanin hakan.
  2. Kokwanto ba ya tasiri a kan alwala, mai sallah yana kan abin yake a kan tsarkinsa muddin dai bai tabbatar da kari (hadasi) ba.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 276) (362)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (8/ 374)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 608).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ƘA'IDOJI NA FIƘHU DA NA USULU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com