Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ، مَنْ ضَارَّ ضَرَّهُ اللَّهُ، وَمَنْ شَاقَّ شَقَّ اللَّهُ عَلَيْهِ».
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa".
Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, baya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida. Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta sai dai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana narko da faruwar cuta ga wanda yake cutar da mutane, da kuma faruwar wahala ga wanda yake tsanantawa mutane.

Fa’idoji
  1. Hani game da ramuwa da sama da abin da aka yi.
  2. Allah bai umarci bayainsa da wani abu da zai cutar da su ba.
  3. Haramta cuta da cutarwa ta magana ko da aiki ko da bari.
  4. Sakamako yana kasancewa daga jinsin aiki, wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cuta, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawa.
  5. Daga ƙa'idojin shari'a akwai: "Cuta ana gusar da ita", shari'a ba ta tabbatar da cuta, kuma tana inkarin cutarwa.
Madogara

سنن الدارقطني (4/ 51) (3079). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص74). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص325). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص112).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ƘA'IDOJI NA FIƘHU DA NA USULU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com