Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu cuta ba cutarwa

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ سَعْدِ بْنِ مَالِكِ بْنِ سِنَانٍ الخُدْرِيّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ».
Daga Abu Sa'id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Babu cuta ba cutarwa».
Ibnu Majah da Darakutni da wasunsu Suka ruwaito shi a matsayin MusnadDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, ba ya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida. Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta saidai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba.

Fa’idoji
  1. Hani game da ramuwa da sama da abin da aka yi.
  2. Allah bai umarci bayainsa da wani abu da zai cutar da su ba.
  3. Hadisin ƙa'idace mai girma a haramcin cuta, cutarwa kuma tana kasancewa ne da magana ko aiki ko da barin (yin abu).
  4. Daga ƙa'idojin shari'a akwai: "Cuta ana gusar da ita", shari'a ba ta tabbatar da cuta, kuma tana inkarin cutarwa.
Madogara

سنن الدارقطني (4/ 51) (3079). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص74). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص325). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص112).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ƘA'IDOJI NA FIƘHU DA NA USULU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com