Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يَنْظُرُ اللهُ إِلَى رَجُلٍ أَتَى رَجُلًا أَوِ امْرَأَةً فِي دُبُرٍ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura".
Tirmizi da Nasa'i a cikin Al-kubra ne Suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana narko mai tsanani da cewa Allah ba Ya duba duban rahama zuwa namijin da ya zo wa namiji ta duburarsa ko mace ta duburarta, kuma hakan laifi ne babba daga cikin manyan laifuka.

Fa’idoji
  1. Zakkewa namiji ga namiji - shi ne liwaɗi - yana daga manyan zunubai.
  2. Zakkewa mace ta duburarta yana daga manyan zunubai.
  3. (Allah ba Ya duba) wato duba na rahama da tausayi, ba ana nufi da shi cewa: Duba gamamme ba; domin Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - wani abu ba ya ɓoyuwa gare Shi kuma wani abu ba ya fakuwa daga ganinSa.
  4. Waɗannan ayyukan suna daga manyan (ayyukan) alfasha kuma mafi haɗarinsu akan mutuntaka; dan abinda ke cikinsu na saɓawa nagartacciyar ɗabi'a ta mutuntaka, da ƙarancin zuriya, da ɓa ta rayuwar auratayya, da dasa ƙiyayya da gaba, da afkawa a wuraren ƙazanta.
Madogara

سنن الترمذي (2/ 457) (1165). السنن الكبرى للنسائي (8/ 197) (8952). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (5/ 347). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (4/ 536). تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، للمباركفوري (4/ 276).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCEN TA'AZIRI (JAN KUNNE)

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com