عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: سُئل رسول الله صلى الله عليه وسلم عن الخمر تُتَّخَذُ خَلًّا؟ قال: «لا».
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi an tambaye shi game da giya da ake daukanta a matsayin tsumi? sai ya ce: A'a
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Anas bin Malik - Allah ya yarda da shi - ya ba da labarin cewa an tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da hukuncin giya idan an sha shi har sai ya zama ruwan tsami, kuma wannan ya kasance bayan haramcin an bayyana giya, kuma ya hana hakan. A kan wannan, idan giya ta rikide ta zama ruwan tsami ta kowace hanya, walau ta hanyar sanya wani abu a ciki kamar su burodi, albasa, yisti, dutse da makamantansu, ko kuma motsa shi daga inuwa zuwa rana ko akasin haka, ko kuma ta cakuɗa da wani sinadarin, to haramun ne, kuma wannan jujjuyawar ba ta canza shi daga hukuncinsa ba .. Ta shiga kanta ba tare da wani ya yi aiki ba, don haka sai ta tsarkake kanta kuma an halatta ta
Madogara
- صحيح مسلم، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
- سبل السلام شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن إسماعيل بن صلاح الصنعاني، الناشر: دار الحديث, بدون طبعة وبدون تاريخ.
- توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م
- نيل الأوطار, محمد بن علي بن محمد بن عبد الله الشوكاني اليمني, تحقيق: عصام الدين الصبابطي, دار الحديث، مصر, الطبعة: الأولى، 1413هـ - 1993م.
- منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن صالح الفوزان، الناشر : دار ابن الجوزي الطبعة : الأولى ، 1427 هـ - 1431 هـ
- فتاوى اللجنة الدائمة - المجموعة الأولى, اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء, جمع وترتيب: أحمد بن عبد الرزاق الدويش, الناشر: رئاسة إدارة البحوث العلمية والإفتاء - الإدارة العامة للطبع – الرياض.
- تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427 ه - 2006 م.
- فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام لمحمد بن صالح بن محمد العثيمين، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة، ط1، المكتبة الإسلامية، مصر، 1427ه.
- بلوغ المرام من أدلة الأحكام، لابن حجر. دار القبس للنشر والتوزيع، الرياض - المملكة العربية السعودية. الطبعة: الأولى، 1435 هـ - 2014 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن ابن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «كل مُسْكِرٍ خَمْرٌ، وكل مُسْكِرٍ حرام، ومن شرِب الخمر في الدنيا فمات وهو يُدْمِنُهَا لَمْ يَتُبْ، لَمْ يَشْرَبْهَا في الآخرة».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba".
Muslim ne ya ruwaito shi, shi kuwa Bukhari ya ruwaito jimla ta karshe ne ta HadisinDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abinda yake kawar da hankali kuma ya tafiyar da shi to shi giya ne mai sa maye daidai ne ya kasance sha ne ko ci ko shaƙa ko makamancin hakan, kuma dukkan abinda yake sa maye kuma ya kawar da hankali to haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta shi kuma Ya yi hani daga gare shi, ƙanƙaninsa da mai yawansa. Kuma dukkan wanda ya sha kowanne nau'i daga Nau’ukan waɗannan masu sa mayen, kuma ya lazimci shansu bai tuba ba daga gare su har ya mutu; to shi ya cancanci uƙubar Allah ta hanyar haramta masa shan ta a aljanna.
Fa’idoji
- Illar haramta giya shi ne maye, dukkan abinda yake sa maye daga kowanne nau'i ya kasance to haramun ne.
- Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
- Shan giya a cikin aljanna yana daga cikar jin daɗi da cikar ni'ima.
- Wanda bai kame kansa daga shan giya a duniya ba Allah Zai haramta masa shan ta a cikin aljanna. Sakamako yana zuwa ne daga jinsin aiki.
- Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba daga zunubai kafin mutuwa.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 104) (5575).
صحيح مسلم (3/ 1587) (2003).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 519).
فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 418).
توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (6/ 307).
معالم السنن، وهو شرح سنن أبي داود، للخطابي (4/ 264).
الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني، للساعاتي (16/ 116).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 30).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (6/ 2382).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنْتُ سَاقِيَ القَوْمِ فِي مَنْزِلِ أَبِي طَلْحَةَ، وَكَانَ خَمْرُهُمْ يَوْمَئِذٍ الفَضِيخَ، فَأَمَرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُنَادِيًا يُنَادِي: أَلاَ إِنَّ الخَمْرَ قَدْ حُرِّمَتْ، قَالَ: فَقَالَ لِي أَبُو طَلْحَةَ: اخْرُجْ، فَأَهْرِقْهَا، فَخَرَجْتُ فَهَرَقْتُهَا، فَجَرَتْ فِي سِكَكِ المَدِينَةِ، فَقَالَ بَعْضُ القَوْمِ: قَدْ قُتِلَ قَوْمٌ وَهِيَ فِي بُطُونِهِمْ، فَأَنْزَلَ اللَّهُ: {لَيْسَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جُنَاحٌ فِيمَا طَعِمُوا} [المائدة: 93] الآيَةَ.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Na kasance ina shayar da mutane ( giya) a gidan Abu Ɗalha, kuma giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, sai a (Cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yan dabino kafin su zama ɗanye) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wani mai kira ya yi kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai ta kwaranya a lungunan Madina, sai wasu cikin mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe wasu mutane alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka ɗanɗana} [al-Ma'ida: 93] karanta ayar har ƙarshenta.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana cikin shayar da wanda yake cikin gidan mijin babarsa Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi -, giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, shi ne cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yansa kafin ya zama ɗanye, sai ga mai kira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita, ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai giyar ta kwarara a lungunan Madina, sai wasu daga mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe (a jihadi) wasu sahabbai kafin haramtata alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da:
{Babu laifi akan waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka dandana} [al-Ma'ida: 93] Aya. Wato: Babu zunubi akan waɗanda suka yi imani a cikin abinda suka dandana kuma suka sha na giya kafin haramtata.
Fa’idoji
- Falalar Abu Ɗalha da sahabbai - Allah Ya yarda da su -, dan sun amsa umarnin Allah da gaggawa kuma ba tare da tambaya ba, wannan shi ne abinda ya kamata ga musulmi na gaskiya.
- Giya: Ita Suna ne da ya ƙunshi dukkan abin da yake sa maye.
- Fadikh: wani abin sha ne da ake yinsa daga 'ya'yan dabino da kuma bushasshensa ba tare da wuta ta taɓa shi ba, Busr kuwa: Shi ne 'ya'yan dabino kafin ya zama ɗanye.
- Ibnu Hajar ya ce: Muhallab ya ce: Kawai an zubar da giyar ne a hanya dan bayyanar da ƙiyayyarta da kuma bayyanar da barinta, hakan ya fi rinjaye a maslaha daga cutuwa da zubar da ita a hanya.
- Bayanin rahamar Allah ga bayinSa, kuma cewa Shi ba Ya yin hisabi akan aiki kafin saukar da hukunci.
- Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta giya; dan abinda ke cikinta na nau’ukan barna da zasu sa cuta ga hankali da kuma dukiya, saboda da ita ne mutum yake aikata zunubai da yawa; dan gushewar hankalinsa.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 132) (2464).
صحيح مسلم (3/ 1570) (1980).
النهاية في غريب الحديث والأثر (709) (1006).
فتح الباري لابن حجر (1/ 133).
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (4/ 267).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا أَسْكَرَ كَثِيرُهُ فَقَلِيلُهُ حَرَامٌ».
Daga Jabir ɗan Abbdullahi - Allah Ya ƙara yarda a gare su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abin sha ko abin ci da yake kawar da hankali lokacin da aka ci ko aka sha mai yawa daga gare shi, to cin kaɗan daga gare shi abin haramtawa ne koda bai tafiyar da hankali ba.
Fa’idoji
- Kiyayewar shari'a akan hankulan mutane.
- Ingancin lura da toshe kafa, hakan ta hanyar kulle dukkan abinda yake kaiwa zuwa waɗannan munanan abubuwan.
- Haramta kaɗan na abinda yake sa maye; domin shi tsani ne ga maye.
- idan kaɗan ɗinsa ko mai yawansa baisa maye ba, to shi ba haramun ba ne.
Madogara
سنن أبي داود (5/ 523) (3681).
سنن الترمذي (3/ 442) (1865).
سنن ابن ماجه (4/ 475) (3393).
مسند أحمد (23/ 51) (14703).
فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام (5/ 418).
شرح سنن أبي داود للعباد (417/ 9).
النهاية في غريب الحديث والأثر (437).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي بُرْدَةَ، عَنْ أَبِيهِ أَبِي مُوسَى الأَشْعَريِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَعَثَهُ إِلَى اليَمَنِ، فَسَأَلَهُ عَنْ أَشْرِبَةٍ تُصْنَعُ بِهَا، فَقَالَ: وَمَا هِيَ؟، قَالَ: «البِتْعُ وَالمِزْرُ»، فَقِيلَ لِأَبِي بُرْدَةَ: مَا البِتْعُ؟ قَالَ: نَبِيذُ العَسَلِ، وَالمِزْرُ: نَبِيذُ الشَّعِيرِ، فَقَالَ: «كُلُّ مُسْكِرٍ حَرَامٌ» خرجه البخاري.
وَخَرَّجَهُ مُسْلِمٌ وَلَفْظُهُ: قَالَ: بَعَثَنِي رَسُولُ اَلله أَنَا وَمُعَاذٌ إِلَى اَليَمَنِ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولُ اَللَّهِ! إِنَّ شَرَابًا يُصْنَعُ بِأَرْضِنَا يُقَال لَهُ: المِزَرُ مِنَ الشَّعِيرِ، وَشَرَابٌ يُقَالُ لَهُ: البِتْعُ مِنَ العَسَلِ، فَقَالَ: «كُلُّ مُسْكِرٍ حَرَامٌ».
وَفِي رِوَايَةٍ لِمُسْلِمٍ: «فَقَالَ: كُلُّ مَا أَسْكَرَ عَنِ الصَّلَاةِ فَهُوَ حَرَامٌ».
وَفِي رِوَايَةٍ لَهُ: «وَكَانَ رَسُولُ الله قَدْ أُعْطِيَ جَوَامِعَ الكَلِمِ بِخَوَاتِمِهِ، فَقَالَ: أَنْهَى عَنْ كُلِّ مُسْكِرٍ أَسْكَرَ عَنْ الصَّلَاةِ».
Dada Abu Burdah, daga babansa Abu Musa al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi -: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aike shi Yaman, sai ya tambaye shi game da wasu wasu abubun sha waɗanda ake yi su a can, sai ya ce: Waɗanne ne su?, ya ce: «Bit'u da Mirzu». Sai akacewa Abu Burda: Menene Bit'u? Ya ce: Tsimin zuma, Mirzu kuma: Tsimin sha'ir (karamar shinkafa), sai ya ce: «Duk abin da yake sa maye haramun ne» Bukhari ne ya fitar da shi. Kuma Muslim ya fitar da shi da lafazin:
Ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni ni da Mu'az zuwa Yaman, sai na ce: Ya Manzon Allah! Lallai akwai wani abin shan da ake yi sa a ƙasarmu ana ce masa: Mirzu daga sha'ir ne, (karanar Shinkafa) da kuma wani abin shan da ake ce masa: Bit'u daga zuma ne, sai ya ce: «Duk abin da yake sa maye haramun ne». A cikin wata riwaya ta Muslim: «Sai ya ce: Duka abin da yasa maye ga sallah to shi haramun ne». A cikin wata riwayar tasa kuma: «Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance haƙiƙa an ba shi matattaran kalmomi da cikarsu, sai ya ce: Ya hana duk abin da yake sa maye wanda ya bugar lokacin sallah».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abu Musa al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aike shi Yaman, sai ya tambaye shi game da wasu kayan shaye-shaye waɗanda ake yin su a can, shin su haramun ne, sai ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da su. Sai Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Shi ne Bit'u: Tsimin zuma, da Mirzu: Tsimin shinkafa. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce alhali ya kasance haƙiƙa an ba shi matattaran kalmomi: «Duk abin da yake sa maye haramun ne».
Fa’idoji
- Tsimi; Shi ne ruwan da ake zuba dabino a cikinsa ko zuma ko sha'ir (karamar Shinkafa) da makamantansu; sai ya bada ɗanɗano na abin sha mai zaƙi, amma bayan haka zai iya zama giya ya zama mai bugarwa.
- Hadisin wata ƙa'iada ce a cikin haramta dukkanin nau'ikan abubuwan da suke sa maye kamar giya da hashish da wasunsu.
- Muhimmancin tambaya game da abin da musulmi yake buƙatuwa zuwa gare shi .
- Farkon lokacin da aka fara haramta giya ya kasance lokacin sallah ne, lokacin da wani daga cikin Muhajirun ya yi sallah, sai ya yi karatu a cikin sallarsa sai ya yi galaɗI (kuskure) a cikin karatunsa; sai faɗinSa Allah - Maɗaukakin sarki - ya sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku kusanci sallah alhali ku kuna cikin maye, har sai kun san abin da kuke faɗa} [al-Nisa'i: 43]. Sai wani mai shela daga cikin masu shelan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kira: Kada mai maye ya kusanci sallah. Sannan Allah Ya haramta ta kwata-kwata da faɗinSa: {Yaku waɗanda suka yi imani kaɗai giya da caca da gumaka da kibau na neman sa'a, ba komai bane sai ƙazanta daga aikin Shaiɗan, dan haka ku nisance su domin ku samu rabauta} [al-ma'ida: 90,91].
- Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
- abin lura a cikin haramcin shi ne samuwar siffar bugarwa; idan tsimi ya siffantu da bugarwa to shi ma haramun ne, idan kuma bai siffantu da bugarwa ba to shi halal ne.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 104) (5575).
صحيح مسلم (3/ 1587) (2003).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 519).
فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 418).
توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (6/ 307).
معالم السنن، وهو شرح سنن أبي داود، للخطابي (4/ 264).
الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني، للساعاتي (16/ 116).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 30).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (6/ 2382).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com