Abu Musa al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aike shi Yaman, sai ya tambaye shi game da wasu kayan shaye-shaye waɗanda ake yin su a can, shin su haramun ne, sai ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da su. Sai Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Shi ne Bit'u: Tsimin zuma, da Mirzu: Tsimin shinkafa. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce alhali ya kasance haƙiƙa an ba shi matattaran kalmomi: «Duk abin da yake sa maye haramun ne».
- Tsimi; Shi ne ruwan da ake zuba dabino a cikinsa ko zuma ko sha'ir (karamar Shinkafa) da makamantansu; sai ya bada ɗanɗano na abin sha mai zaƙi, amma bayan haka zai iya zama giya ya zama mai bugarwa.
- Hadisin wata ƙa'iada ce a cikin haramta dukkanin nau'ikan abubuwan da suke sa maye kamar giya da hashish da wasunsu.
- Muhimmancin tambaya game da abin da musulmi yake buƙatuwa zuwa gare shi .
- Farkon lokacin da aka fara haramta giya ya kasance lokacin sallah ne, lokacin da wani daga cikin Muhajirun ya yi sallah, sai ya yi karatu a cikin sallarsa sai ya yi galaɗI (kuskure) a cikin karatunsa; sai faɗinSa Allah - Maɗaukakin sarki - ya sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku kusanci sallah alhali ku kuna cikin maye, har sai kun san abin da kuke faɗa} [al-Nisa'i: 43]. Sai wani mai shela daga cikin masu shelan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kira: Kada mai maye ya kusanci sallah. Sannan Allah Ya haramta ta kwata-kwata da faɗinSa: {Yaku waɗanda suka yi imani kaɗai giya da caca da gumaka da kibau na neman sa'a, ba komai bane sai ƙazanta daga aikin Shaiɗan, dan haka ku nisance su domin ku samu rabauta} [al-ma'ida: 90,91].
- Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
- abin lura a cikin haramcin shi ne samuwar siffar bugarwa; idan tsimi ya siffantu da bugarwa to shi ma haramun ne, idan kuma bai siffantu da bugarwa ba to shi halal ne.
صحيح البخاري (7/ 104) (5575). صحيح مسلم (3/ 1587) (2003). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 519). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 418). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (6/ 307). معالم السنن، وهو شرح سنن أبي داود، للخطابي (4/ 264). الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني، للساعاتي (16/ 116). فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 30). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (6/ 2382).