Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba

عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «كل مُسْكِرٍ خَمْرٌ، وكل مُسْكِرٍ حرام، ومن شرِب الخمر في الدنيا فمات وهو يُدْمِنُهَا لَمْ يَتُبْ، لَمْ يَشْرَبْهَا في الآخرة».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba".
Muslim ne ya ruwaito shi, shi kuwa Bukhari ya ruwaito jimla ta karshe ne ta HadisinDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abinda yake kawar da hankali kuma ya tafiyar da shi to shi giya ne mai sa maye daidai ne ya kasance sha ne ko ci ko shaƙa ko makamancin hakan, kuma dukkan abinda yake sa maye kuma ya kawar da hankali to haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta shi kuma Ya yi hani daga gare shi, ƙanƙaninsa da mai yawansa. Kuma dukkan wanda ya sha kowanne nau'i daga Nau’ukan waɗannan masu sa mayen, kuma ya lazimci shansu bai tuba ba daga gare su har ya mutu; to shi ya cancanci uƙubar Allah ta hanyar haramta masa shan ta a aljanna.

Fa’idoji
  1. Illar haramta giya shi ne maye, dukkan abinda yake sa maye daga kowanne nau'i ya kasance to haramun ne.
  2. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
  3. Shan giya a cikin aljanna yana daga cikar jin daɗi da cikar ni'ima.
  4. Wanda bai kame kansa daga shan giya a duniya ba Allah Zai haramta masa shan ta a cikin aljanna. Sakamako yana zuwa ne daga jinsin aiki.
  5. Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba daga zunubai kafin mutuwa.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 104) (5575). صحيح مسلم (3/ 1587) (2003). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 519). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 418). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (6/ 307). معالم السنن، وهو شرح سنن أبي داود، للخطابي (4/ 264). الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني، للساعاتي (16/ 116). فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 30). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (6/ 2382).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ABUBUWAN SHA NA HARAMUN

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com