عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت: دَخَلَتْ هِنْدٌ بِنْتُ عُتْبَةَ امْرَأَةُ أَبِي سُفْيَانَ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَتْ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ أَبَا سُفْيَانَ رَجُلٌ شَحِيحٌ، لَا يُعْطِينِي مِنَ النَّفَقَةِ مَا يَكْفِينِي وَيَكْفِي بَنِيَّ إِلَّا مَا أَخَذْتُ مِنْ مَالِهِ بِغَيْرِ عِلْمِهِ، فَهَلْ عَلَيَّ فِي ذَلِكَ مِنْ جُنَاحٍ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خُذِي مِنْ مَالِهِ بِالْمَعْرُوفِ مَا يَكْفِيكِ وَيَكْفِي بَنِيكِ».
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Hindu 'yar Utbatah - matar Abu Sufyan- ta shigo wajen Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ta ce:
Ya Manzon Allah, Abu Sufyan ya kasance mutum ne mai ƙwauro, ba ya bamu abin da zai ishe mu ni da 'ya'ya na sai abinda na ɗauka daga cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba, shin ba laifi akaina a yin hakan? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Hindu 'yar Utbah - Allah Ya yarda da ita - ta nemi fatawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mijinta Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi -, kuma shi mutum ne marowaci mai kwaɗayin dukiyarsa, ba ya bata abinda zai isheta ya ishi 'ya'yanta na ciyarwa, sai dai in ta ɗauka a ɓoye cikin dukiyarsa alhali shi bai sani ba, shin akwai wani laifi akanta a hakan? Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ki ɗauki gwargwadan abinda aka sani a al'ada cewa shi zai isa cikin dukiyarsa koda ba tare da saninsa ba.
Fa’idoji
- Wajabcin ciyar da mata da kuma 'ya'ya.
- Ibnu Hajar ya ce: Abin nufi a faɗinsa: "Ki ɗauki abinda zai isheki cikin dukiyarsa ta yadda al'ada take gudana da shi", sai ya mayar da ita zuwa ga al'ada a cikin abinda babu iyakancewar shari'a a cikinsa.
- Ibnu Hajar ya ce: An kafa hujja da wanna hadisin akan halaccin ambatan mutum da abinda ba ya ƙayatar da shi idan ya kasance ta fuskar neman fatawa ne da kai ƙara da makamancin haka, kuma shi ne ɗaya daga cikin guraren da aka halatta giba (yi da mutum) a cikinsu.
- AlƘurɗubi ya ce: Hindu bata nufin siffanta Abu Sufyan da ƙwauro a dukkanin halayensa, kawai ta siffanta halinta ne tare da shi kuma cewa shi yana yi mata ƙwauro ita da 'ya'yanta, wannan ba ya lazimtar rowa kai tsaye, domin cewa mafi yawancin shugabanni sunayin haka tare da iyalansu suna fifita na waje dan jawo zukatansu.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 79) (2211).
صحيح مسلم (3/ 1338) (1714).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص700).
الإعلام بفوائد عمدة الأحكام، لابن الملقن (10/ 12).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن كَعْب بن مالك رضي الله عنه قال: قلتُ: يا رسولَ الله، إن مِن تَوبتي أن أَنْخَلِعَ مِنْ مالي؛ صدقةً إلى الله وإلى رسولِه، فقال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم : "أمسِكْ عليك بعضَ مالِكَ؛ فهو خيرٌ لكَ".
Daga Ka'ab Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya ce: na ce: ya manzon Allah lallai ne daga cikin tuba na in rabu da dukkan Dukiya ta; Sadaka saboda Allah da Manzon sa, sai manzon Allah SAW ya ce: "Ka riqe wani vangaren na dukiyarka yafi maka Al-kairi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
-صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه.
-صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.
-عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ.
-تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414ه.
-تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ.
-الإلمام بشرح عمدة الأحكام, إسماعيل الأنصاري, الطبعة الثانية 1392هـ.
-الشرح الممتع على زاد المستقنع، محمد بن صالح بن محمد العثيمين، دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى، 1422- 1428هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ وَهُوَ عَلَى المِنْبَرِ، وَذَكَرَ الصَّدَقَةَ، وَالتَّعَفُّفَ، وَالمَسْأَلَةَ: «اليَدُ العُلْيَا خَيْرٌ مِنَ اليَدِ السُّفْلَى، فَاليَدُ العُلْيَا: هِيَ المُنْفِقَةُ، وَالسُّفْلَى: هِيَ السَّائِلَةُ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce akan minbari, kuma sai ya ambaci sadaka, da kamewa, da kuma roƙo: «Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci, hannu maɗaukaki: Shi ne mai ciyarwa (mai bayarwa) maƙasƙanci kuma: Shi ne mai roƙo».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambata alahali yana huɗubar akan sadaka da kamewa daga roƙo akan minbari; sannan ya ce: Hannau maɗaukaki mai ciyarwa mai bayarwa shi ne nafi alheri kuma mafi soyuwa a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo.
Fa’idoji
- A cikinsa akwai falalar bayarwa da kuma ciyarwa a hanyoyin alheri da kuma zargin roƙo.
- A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan kamewa daga roƙo da kuma wadatuwa daga mutane, da kwaɗaitarwa akan kyawawan al'amura, da barin komabayansu, Allah Yana son kyawawan al'amura.
- Hannaye guda huɗu ne, su a falala kamar yadda yake tafe ne: Maɗaukakinsu mai ciyarwa, sannan mai kamewa daga karɓa, sannan mai karɓa ba tare da roƙo ba, sannan komkabayansu shi ne mai roƙo.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 112) (1429).
صحيح مسلم (2/ 717) (1033).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 590).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 465).
التوضيح لشرح الجامع الصحيح، لابن الملقن (10/ 315).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 388).
تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، المباركفوري (3/ 288).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص212).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أم سلمة رضي الله عنها ، قالت: قلت: يا رسول الله، هل لي أجرٌ في بني أبي سلمة أن أُنْفِقَ عليهم، ولستُ بتاركتهم هكذا وهكذا إنما هم بَنِيَّ؟ فقال: «نعم، لك أجرُ ما أنفقتِ عليهم».
A kan Ummu Salamah - Allah ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah, shin ina da lada ga ‘ya’yan Abi Salamah da zan ciyar da su, kuma ban bar su haka da sauransu da sauransu ba amma su‘ ya’ya na ne? Ya ce: "Na'am, za a ba ku ladar abin da kuka ciyar a kansu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ummu Salamah, Allah ya yarda da ita, ta ce wa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Shin ina da wani lada a ciki na ciyar da ‘ya’yana daga Abu Salamah kuma na isar musu, kuma ban bari su watse a cikin neman guzuri ba? Ko kuwa babu wani sakamako a wurina saboda na yi ta ne da tausayi saboda 'ya'yana ne? Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gaya mata cewa za a ba ta ladan ciyarwa a kan su.
Madogara
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي.
صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي، بيروت.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «قَالَ اللهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ أُنْفِقْ عَلَيْكَ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin Allah maɗaukakin sarki Ya ce: Ya kai Ɗan Adam ka ciyar cikin ciyarwar wajibi da ta Mustahabbi zan yalwata maka, zan kuma ba ka makwafin abin da ka bayar, kuma in sanya maka albarka.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa a kan sadaka da kuma ciyarwa Fi-sabilillahi.
- Ciyarwa ta ɓangarorin alheri yana daga cikin manyan dalilan samun albarka a arziki da kuma ninka shi, da kuma yadda Allah zai mayarwa bawa abin da ya ciyar.
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaitoshi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen Alkur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karantashi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 62) (5352).
صحيح مسلم (2/ 690) (993).
شرح النووي على مسلم (7/ 79).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 603).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قالَ: قالَ رَسُولُ اللَّهِ صلَّى اللَّهُ عليْه وسلَّمَ: «دِينَارٌ أَنْفَقْتَهُ فِي سَبِيلِ اللهِ، وَدِينَارٌ أَنْفَقْتَهُ فِي رَقَبَةٍ، وَدِينَارٌ تَصَدَّقْتَ بِهِ عَلَى مِسْكِينٍ، وَدِينَارٌ أَنْفَقْتَهُ عَلَى أَهْلِكَ أَعْظَمُهَا أَجْرًا الَّذِي أَنْفَقْتَهُ عَلَى أَهْلِكَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye (‘yanta baiwa), da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; to mafi girman su a lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci sashin nau’ukan ciyarwa, sai ya ce: Dinarin da ka ciyar da shi a yaƙi a tafarkin Allah, da dinarin da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye da bauta, da dinarin da ka yi sadaka ga miskini mabuƙaci, da dinarin da ka ciyar da shi ga iyalanka, sannan ya bada labarin cewa mafi girmansu a lada a wajen Allah shi ne wanda ka ciyar da shi ga iyalanka da wanda ciyar da shi ya lazimceka.
Fa’idoji
- Yawan ƙofofin ciyarwa a tafarkin Allah.
- Gabatar da abin da ya fi a cikin babin ciyarwa a lokacin cinkoso, yana daga hakan ciyarwa ga iyali a lokacin da ciyarwa ga gabaɗayan ba zai yi wu ba.
- Nawawi ya faɗa a Sharhin Muslim: Kwaɗaitarwa akan ciyarwa ga iyalai, da kuma bayanin girman lada a cikinta; domin daga cikinsu akwai wanda ciyarwarsa take wajaba ta hanyar kusanci, daga cikinsu akwai wanda take zama mustahabbi kuma tana zama sadaka da sada zumunci, kuma daga cikinsu akwai wadda take zama wajiba ta hanyar mallakar aure ko mallakar dama (bayi), wannan dukkansa mai falala ne kuma abin kwaɗaitarwa ne a kansa, kuma shi ya fi sadakar nafila.
- Sindi ya ce: Faɗinsa: (Dinaren da yake ciyar da shi ga iyalansa), wato: Idan ya yi hakan don Allah kuma ya yi nufin haƙƙin iyalai misali.
- Abu Kilaba ya ce; Wane mutum ne mafi girman lada daga mutumin da yake ciyarwa ga iyalai ƙanana da zai karesu ko Allah Ya anfanar da su da shi kuma ya wadata su?!
Madogara
صحيح مسلم (2/ 692) (995).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 156).
نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 291).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 374).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص209).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي مسعود رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إِذَا أَنْفَقَ الرَّجُلُ عَلَى أَهْلِهِ يَحْتَسِبُهَا فَهُوَ لَهُ صَدَقَةٌ».
Daga Abu Mas’ud Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bada rabarin cewa idan mutum ya ciyar da iyalinsa waɗanda ciyarwarsu ta wajaba a kansa, kamar matarsa da iyayensa da ‘ya’yansa da sauransu, yana mai neman kusanci zuwaga Allah da hakan, yana neman ladan ciyarwar a wurin Allah, to, Allah zai ba shi ladan sadakarsa.
Fa’idoji
- Samun lada idan aka ciyar da iyali.
- Mumini [na gaskiya] yana neman yardar Allah a aikinsa da kuma lada da sakamakon da yake wurin Allah.
- Ya kamata a halarto da niyya mai kyau a kowanne aiki, daga cikin hakan akwai lokacin ciyar da iyali.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 20) (55).
صحيح مسلم (2/ 695) (1002).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 334).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 157).
نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن وغيره (1/ 293).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، سليم الهلالي (1/ 375).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لا يَقْتَسِمُ وَرَثَتي دينارًا ولا درهمًا، ما تَرَكْتُ بَعْدَ نَفَقَة نسائي، ومئونَة عامِلي فهو صَدَقة».
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Ba'a rabawa Magadana ko dinare daya ko Dirhami abunda na bari bayan abincin Iyalina, da ladan Ma'aikata na to sauran Sadaka ne"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wannan Hadisn yana nuna cewa Magadan Manzon Allah SAW ba zasu raba -bayan Mutuwarsa- wani dinare ko irhami daga Dukiyarsa ba; Saboda Shi SAW yana daga cikin Annabawa kuma Annabawa basa gadar da Zinare ko Dirhami; Saboda su basa basa tara Duniya, Kuma kaxai Saqonsu shi ne shiryar da Mutane, to idan aka samu Wata Dukiya bayan Mutuwarsa to abincin Matansa ne, haka kuma na Halifansa ne bayansa, ko kuma duk wanda yake jagorantar Musulmai bayansa, kuma duk abunda ya karu kan hakan to sadaka ne
Madogara
- صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه.
- صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
- شرح صحيح البخاري لابن بطال، تحقيق: أبي تميم ياسر بن إبراهيم، نشر: مكتبة الرشد، الرياض-السعودية، الطبعة: الثانية 1423ه، 2003م.
- إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري، لأحمد بن محمد بن أبى بكر بن عبد الملك القسطلاني القتيبي المصري، الناشر: المطبعة الكبرى الأميرية، مصر، الطبعة: السابعة، 1323 هـ.
- عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لمحمود بن أحمد بن موسى الحنفى بدر الدين العينى، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
- مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com