Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ وَهُوَ عَلَى المِنْبَرِ، وَذَكَرَ الصَّدَقَةَ، وَالتَّعَفُّفَ، وَالمَسْأَلَةَ: «اليَدُ العُلْيَا خَيْرٌ مِنَ اليَدِ السُّفْلَى، فَاليَدُ العُلْيَا: هِيَ المُنْفِقَةُ، وَالسُّفْلَى: هِيَ السَّائِلَةُ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce akan minbari, kuma sai ya ambaci sadaka, da kamewa, da kuma roƙo: «‌Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci, hannu maɗaukaki: Shi ne mai ciyarwa (mai bayarwa) maƙasƙanci kuma: Shi ne mai roƙo».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambata alahali yana huɗubar akan sadaka da kamewa daga roƙo akan minbari; sannan ya ce: Hannau maɗaukaki mai ciyarwa mai bayarwa shi ne nafi alheri kuma mafi soyuwa a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo.

Fa’idoji
  1. A cikinsa akwai falalar bayarwa da kuma ciyarwa a hanyoyin alheri da kuma zargin roƙo.
  2. A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan kamewa daga roƙo da kuma wadatuwa daga mutane, da kwaɗaitarwa akan kyawawan al'amura, da barin komabayansu, Allah Yana son kyawawan al'amura.
  3. Hannaye guda huɗu ne, su a falala kamar yadda yake tafe ne: Maɗaukakinsu mai ciyarwa, sannan mai kamewa daga karɓa, sannan mai karɓa ba tare da roƙo ba, sannan komkabayansu shi ne mai roƙo.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 112) (1429). صحيح مسلم (2/ 717) (1033). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 590). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 465). التوضيح لشرح الجامع الصحيح، لابن الملقن (10/ 315). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 388). تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، المباركفوري (3/ 288). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص212).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SADAKA TA NAFILA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com