عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «قَالَ اللهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ أُنْفِقْ عَلَيْكَ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin Allah maɗaukakin sarki Ya ce: Ya kai Ɗan Adam ka ciyar cikin ciyarwar wajibi da ta Mustahabbi zan yalwata maka, zan kuma ba ka makwafin abin da ka bayar, kuma in sanya maka albarka.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa a kan sadaka da kuma ciyarwa Fi-sabilillahi.
- Ciyarwa ta ɓangarorin alheri yana daga cikin manyan dalilan samun albarka a arziki da kuma ninka shi, da kuma yadda Allah zai mayarwa bawa abin da ya ciyar.
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaitoshi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen Alkur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karantashi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 62) (5352). صحيح مسلم (2/ 690) (993). شرح النووي على مسلم (7/ 79). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 603).