Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’ar daga gareta

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي لله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يَفْرَكْ مُؤْمِنٌ مُؤْمِنَةً، إِنْ كَرِهَ مِنْهَا خُلُقًا رَضِيَ مِنْهَا آخَرَ» أَوْ قَالَ: «غَيْرَهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’ar daga gareta Ko ya ce: "Waninsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana miji ya ki matarsa ƙin da zai kai zuwa ga zalinci da barinta da bijire mata; Domin mutum an halicce shi ne akan tawaya, idan ya ki wata mummunar ɗabi'a daga gareta, to zai samu wata kyakkyawar ɗabi'ar a tare da ita; sai ya yarda da mai kyan da ta dace da shi, kuma ya yi haƙuri akan wadda bai yarda ba ta munanar, abinda zai sa shi ya yi haƙuri kada ya ki ta ƙiyayyar da zata ɗauke shi akan rabuwa da ita.

Fa’idoji
  1. Kiran mumini zuwa adalci da hukuncin hankali a kowanne saɓanin da ya faru tare da matarsa, da rashin komawa zuwa hukuncin zuciya da fusatar wani ɗan lokaci.
  2. Sha'anin mumini kada ya ki mumina ƙiyayya baki ɗaya da zata ɗauke shi akan rabuwa da ita, kai abinda ya kamata akansa ya kau da kai daga abinda yake ƙi dan abinda yake so.
  3. Kwaɗaitarwa akan kyakkyawan mu'amala da zamantakewa tsakanin ma'aurata.
  4. Imani mai kira ne ga kyawawan ɗabi'u, mumini da mumina ba sa kaɗaitaka daga kyawawan ɗabi'u; to imani yana lazimtar samun ɗabi'u ababen yabo a cikinsu.
Madogara

صحيح مسلم (2/ 1091) (1469). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 359). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 122). فتح رب البرية بتلخيص الحموية، لابن عثيمين (ص117). مجموع فتاوى ابن باز (25/ 246). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 282).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
AURE

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com