Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Mumini ba zai gusheba a cikin yalwar Addininsa ba, muddin dai bai zubar da jinin da aka haramta masa ba».
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mumini ba zai gushe ba a cikin yalwar ayyukansa na gari, da fatan samun rahamar Allah da gafararSa da kuma rangwaminSa, har sai idan ya kashe wani mutumin da aka haramta masa kashe shi to haƙiƙa ayyukansa zasu yi masa ƙunci; domin ba zasu iya biyan laifin kisa da kuma zunibinsa mai girma ba.
Fa’idoji
Girman kisa ba tare da wani haƙƙi ba da kisa na ganganci, domin yana fitar da mumini daga yalwa a cikin Addini zuwa ƙunci.
Jinanen da aka haramta nau'i huɗu ne: 1- Jinin musulmi, shi ne mafi girmansu. 2- Jinin kafirin amana (Zimmi), su ne Yahudawa da Nasara waɗanda aka tabbatar da su akan addininsu a garin Musulunci ta hanyar bada jizya, da zartar da hunce-hukuncen Musulunci a cikinsu. 3- Jinin kafirin da aka yi yarjejeniya da shi (Mu'ahad), sune kafiran da suke a garuruwansu waɗanda a tsakaninmu akwai sulhu cewa ba zamu yaƙesu ba suma ba zasu yaƙemu ba. 4- Jinin kafiri Musta'amani, shi ne kafirin da ake yaƙi da shi wanda tsakaninmu babu alƙawari, sai dai shugaba ko wanda yake mallakar hakan daga mataimakansa ya amintar da shi a lokaci iyakantacce cewa zai shigo garin musulmai.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 2) (6862).
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (10/ 41).
تطريز رياض الصالحين (ص: 171).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada, wanda ya tsotsi wata gubar sai ya kashe kansa to gubarsa tana hannunsa zai dinga tsotsarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe to ƙarfen zai zama a hannunsa zai dinga cakawa cikinsa shi a cikin wutar Jahannama yana madawwami har abada a cikinta».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi gangancin kashe kansa gargaɗi a duniya cewa za’a yi masa uƙuba a ranar alƙiyama a cikin wutar Jahannama ta irin hanyar da ya yi wa kansa a duniya dan sakamakon da ya dace, wanda ya faɗo daga saman dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wutar Jahannama zai dinga faɗowa a cikinta daga dutsen Jahannama zuwa kwarinta yana madawwami a cikinta, wanda ya kwankwɗi wata guba sai ya kashe kansa da ita to gubarsa tana hannunsa zai dinga kwankwaɗarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya cakawa kansa wani karfe a cikinsa sai ya kashe kansa, to karfensa yana hannunsa zai dinga sukar kansa da shi a cikinsa a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada.
Fa’idoji
Haramcin mutum ya kashe kansa, kuma cewa shi yana daga cikin manyan zunuban da yake cancantar azaba mai raɗaɗi da su.
Abinda ya ambata a cikin hadisin buga misali ne ga wasu daga cikin nau'ikan kashe rai, inba haka ba to ta kowace hanaya ya kashe rai za’a yi masa uƙuba da kwatankwacin abinda ya aikatawa kansa, haƙiƙa faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo a cikin Sahihul Bukhari cewa: «Wanda ya shaƙe kansa zai shaƙe shi a cikin wuta, wanda kuma ya soke kansa to zai sokeshi a cikin wuta».
Nawawi ya ce: Amma faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (To shi yana cikin wutar Jahanama yana madawwami a cikinta har abada); sai aka ce: A cikinsa akwai maganganu, na farkonsu: Cewa shi abin ɗauka ne akan wanda ya aikata hakan yana mai halattawa tare da saninsa da haramcin to wannan kafiri ne, wannan kuma ita ce uƙubarsa. Na biyu: Cewa abin nufi da dawwama ita ce tsawon dadewa da kuma zaman da za'a tsawaita ba wai haƙiƙanin dawwamar ba, kamar yadda ake cewa: Allah Ya dawwamar da mulkin sarki. Na uku: Cewa wannan shi ne sakamakonsa, sai dai (Allah) tsarki ya tabbatar maSa ya daukaka ya yi baiwa sai Ya bada labarin cewa wanda ya mutu yana musulmi ba zai dawwama a cikin wuta ba.
Wannan yana daga babin tabbatar da jinsin uƙubobin lahira ga laifukan duniya, kuma ana fahimta daga gare shi cewa laifin mutum yana kan kansa kamar laifin waninsa ne akan waninsa a zunubi; domin cewa ransa ba mallakinsa bane kai tsaye, kai shi na Allah ne - Maɗaukakin sarki -, ba'a tasarrufi a cikinsa sai da abinda Ya yi masa izini a cikinsa.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 139) (5778).
صحيح مسلم (1/ 103) (109).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (3/ 306).
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (8/ 414).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 310).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (21/ 291).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi ga musulmi ya nuna ɗan uwansa musulmi da kowane irin makami, domin cewa shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya ɗauke shi akan motsa makamin a hannunsa, sai ya kashe ɗan uwansa ko ya cutar da shi, sai ya faɗa cikin saɓon da zai kai shi ya faɗa cikin ramin wuta.
Fa’idoji
Bayanin haramcin jinin musulmi.
Wajabcin girmama musulmi da kiyayewa daga sadar da sharri gare shi ta hanyar aiki ne ko magana, daga hakan akwai nuni da ƙarfe ko da da wasa ne; domin cewa Shaiɗan zai iya zaburar da hannunsa sai ya ƙawata masa dukan ɗan uwansa, ko ya fizge makamin daga hannunsa sai ya faɗa ba tare da zaɓinsa ba sai ya cutar da ɗan uwansa.
Toshe kafa da yin hani daga abinda zai kai zuwa abinda aka haramta.
Kwaɗayi akan zaman lafiyar zamantakewar jama'a da kiyaye alaƙoƙi tsakanin mutane, da rashin tsoratasu koda da nuni ne da kuma yi musu tsawa.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 49) (7072).
صحيح مسلم (4/ 2020) (2617).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (24/ 187).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com