Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mumini ba zai gushe ba a cikin yalwar ayyukansa na gari, da fatan samun rahamar Allah da gafararSa da kuma rangwaminSa, har sai idan ya kashe wani mutumin da aka haramta masa kashe shi to haƙiƙa ayyukansa zasu yi masa ƙunci; domin ba zasu iya biyan laifin kisa da kuma zunibinsa mai girma ba.
- Girman kisa ba tare da wani haƙƙi ba da kisa na ganganci, domin yana fitar da mumini daga yalwa a cikin Addini zuwa ƙunci.
- Jinanen da aka haramta nau'i huɗu ne: 1- Jinin musulmi, shi ne mafi girmansu. 2- Jinin kafirin amana (Zimmi), su ne Yahudawa da Nasara waɗanda aka tabbatar da su akan addininsu a garin Musulunci ta hanyar bada jizya, da zartar da hunce-hukuncen Musulunci a cikinsu. 3- Jinin kafirin da aka yi yarjejeniya da shi (Mu'ahad), sune kafiran da suke a garuruwansu waɗanda a tsakaninmu akwai sulhu cewa ba zamu yaƙesu ba suma ba zasu yaƙemu ba. 4- Jinin kafiri Musta'amani, shi ne kafirin da ake yaƙi da shi wanda tsakaninmu babu alƙawari, sai dai shugaba ko wanda yake mallakar hakan daga mataimakansa ya amintar da shi a lokaci iyakantacce cewa zai shigo garin musulmai.
صحيح البخاري (9/ 2) (6862). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (10/ 41). تطريز رياض الصالحين (ص: 171).