Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 61

At-Tawba 9:61

التوبة

وَمِنْهُمُ ٱلَّذِينَ يُؤْذُونَ ٱلنَّبِىَّ وَيَقُولُونَ هُوَ أُذُنٌ ۚ قُلْ أُذُنُ خَيْرٍ لَّكُمْ يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَيُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِينَ وَرَحْمَةٌ لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنكُمْ ۚ وَٱلَّذِينَ يُؤْذُونَ رَسُولَ ٱللَّهِ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Ma’ana

Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa "Shi kunne[1] ne." Ka ce: "Kunnen alhẽri gare ku, Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku."Kuma waɗanda suke cũtar Manzon Allah sunã da Azãba mai raɗaɗi.

[1] Shi kunne ne, ma'anarsa, kome ka gaya masa Yanã gaskatawa, watau wai ba shi da wãyon gãne gaskiyã da ƙaryã. Sabõda haka Allah Ya ce: Kunnen alheri, watau ya san gaskiya kuma yana gaskata ta, kuma ya san ƙarya, ba ya aiki da ita.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net