Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 8 · Aya ta 48

Al-Anfaal 8:48

الأنفال

وَإِذْ زَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ أَعْمَـٰلَهُمْ وَقَالَ لَا غَالِبَ لَكُمُ ٱلْيَوْمَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَإِنِّى جَارٌ لَّكُمْ ۖ فَلَمَّا تَرَآءَتِ ٱلْفِئَتَانِ نَكَصَ عَلَىٰ عَقِبَيْهِ وَقَالَ إِنِّى بَرِىٓءٌ مِّنكُمْ إِنِّىٓ أَرَىٰ مَا لَا تَرَوْنَ إِنِّىٓ أَخَافُ ٱللَّهَ ۚ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ

Ma’ana

Kuma a lõkacin da Shaiɗan[1] ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne."

[1] Shaiɗan ya fita zuwa ga Ƙuraishãwa a cikin sũrar surãƙ atu bn Mãlik, ya ce musu Yanã tãre da su, kuma shi ne maƙwabcinsu; watau danginsa, Kan'ãnãwa, bã zã su taɓã su ba da yãƙi, a lõkacin da suke yãƙi da Muhammadu. Bãyan haka da ya tafi Badar yã ga Malã'iku, shĩ ne ya kõma bãya, yanã c ewa wai shi yanã tsõron Allah; watau yanã yi wa Ƙuraishãwa izgili; sũ ne bã su tsõron Allah.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Anfaal

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net