Al-Anfaal 8:47
الأنفالوَلَا تَكُونُوا۟ كَٱلَّذِينَ خَرَجُوا۟ مِن دِيَـٰرِهِم بَطَرًا وَرِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۚ وَٱللَّهُ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطٌ
Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu,[1] sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa.
[1] Kada Musulmi su fita zuwa yãƙi da nũna alfahari da kiɗe-kiɗe da giya da mãtã da maganganun alfãsha, kamar yadda Kuraishãwa suka fita zuwa Badar; ku fita da tawãlu'i da zikirin Allah.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net