Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 66 · Aya ta 6

At-Tahrim 66:6

التحريم

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ قُوٓا۟ أَنفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَـٰٓئِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَّا يَعْصُونَ ٱللَّهَ مَآ أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ

Ma’ana

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku[1] (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umarce su, kuma sunã aikata abin da ake umarnin su.

[1] Tsare kai da iyãli daga wuta yanã sãmuwa da shiryar da su da karãtu da nasiha a kan addini. Wannan yanã a cikin kyawun zamantakewa wanda sũrar ke karantarwa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tahrim

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net