Al-Mumtahana 60:13
الممتحنةيَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَتَوَلَّوْا۟ قَوْمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيْهِمْ قَدْ يَئِسُوا۟ مِنَ ٱلْـَٔاخِرَةِ كَمَا يَئِسَ ٱلْكُفَّارُ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْقُبُورِ
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku jiɓinci waɗansu mutãne[1] da Allah Ya yi hushi a kansu. Lalle sun yanke tsammãni daga (rahamar) Lãhira, kamar yadda kãfirai suka yanke tsammãni daga mazõwa[2] kaburbura.
[1] Allah Ya yi Fushi ga duk wanda ya sani kuma ya ƙi aiki da saninsa kamar Yahũdãwa da miyãgun Mãlamai.
[2] Kãfirai ba su yarda da Tãshin Ƙiyãma ba, sabõda haka suke yanke ƙauna daga wanda ya mutu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net