Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 60 · Aya ta 12

Al-Mumtahana 60:12

الممتحنة

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِىُّ إِذَا جَآءَكَ ٱلْمُؤْمِنَـٰتُ يُبَايِعْنَكَ عَلَىٰٓ أَن لَّا يُشْرِكْنَ بِٱللَّهِ شَيْـًٔا وَلَا يَسْرِقْنَ وَلَا يَزْنِينَ وَلَا يَقْتُلْنَ أَوْلَـٰدَهُنَّ وَلَا يَأْتِينَ بِبُهْتَـٰنٍ يَفْتَرِينَهُۥ بَيْنَ أَيْدِيهِنَّ وَأَرْجُلِهِنَّ وَلَا يَعْصِينَكَ فِى مَعْرُوفٍ ۙ فَبَايِعْهُنَّ وَٱسْتَغْفِرْ لَهُنَّ ٱللَّهَ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

Ma’ana

Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya'a a kan bã zã su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma bã su kashe,[1] ya'yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa[2] a tsãkanin hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a, to, ka karɓi mubãya'arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

[1] A zãmanin jãhiliyya sun kashe 'ya'yansu mãtã ta hanya uku, ɗaya sabõda bãkance na addini, na biyu sabõda tsõron talauci; sunã turbuɗe 'ya'ya mãtã a bãyan sun shekara shida, na uku sabõda kunyar haihuwar mace, sai uwa ta yi rãmi, idan ta haifi namiji ta bar shi, idan kuma ta haifi mace, sai ta tũra ta a cikin rãmin ta turbuɗe.
[2] Sunã tsintar yãro su mayar da shi ɗansu, haka kuma maza na yin tabanni, watau mutum ya mai da ɗan wani nãsa kamar yadda har yanzu kãfirai nã yin sa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Mumtahana

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net