Al-Maaida 5:75
المائدةمَّا ٱلْمَسِيحُ ٱبْنُ مَرْيَمَ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ ٱلرُّسُلُ وَأُمُّهُۥ صِدِّيقَةٌ ۖ كَانَا يَأْكُلَانِ ٱلطَّعَامَ ۗ ٱنظُرْ كَيْفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ ٱلْـَٔايَـٰتِ ثُمَّ ٱنظُرْ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ
Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika[1] ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.
[1] Siddĩƙ shi ne mai yawan gaskatãwar Annabãwa, shi ne mafi ɗaukakar daraja a waliyyan Allah, kamar Abubakar siddĩƙ Sahãbin Annabi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net