Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 58

An-Nisaa 4:58

النساء

إِنَّ ٱللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تُؤَدُّوا۟ ٱلْأَمَـٰنَـٰتِ إِلَىٰٓ أَهْلِهَا وَإِذَا حَكَمْتُم بَيْنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحْكُمُوا۟ بِٱلْعَدْلِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِۦٓ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ سَمِيعًۢا بَصِيرًا

Ma’ana

Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ.[1] Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.

[1] Talakãwa mutãne ne mãsu rauni a cikin hannuwan shugabanninsu. Su da dukiyarsu amãnõni ne na Allah a cikin hannuwan shugabanni, saboda haka tsaronsu da dukiyarsu, gwargwadon shari'a, da yin hukunci a tsakaninsu da ãdalci, bãyar da amãna ne ga mãsu ita.Wanda ya bi son zuciyarsa duka ga ɗayan waɗannan abũbuwa, to, yã yi yaudara ga Allah ke nan. Allah kuma zai kama shi da hukuncin mayaudari.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net