Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 115

An-Nisaa 4:115

النساء

وَمَن يُشَاقِقِ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ ٱلْهُدَىٰ وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ ٱلْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِۦ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصْلِهِۦ جَهَنَّمَ ۖ وَسَآءَتْ مَصِيرًا

Ma’ana

Kuma wanda ya sãɓã wa[1] Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma.

[1] Hana fassarar Alƙur'ãni ko sunnar Annabi, ba a kan hanyar da Annabi ko Sahabbansa da waɗanda suka bi hanyarsu suka fassara ba. Da mutum ya yi tãwilin Alƙur'ãni, gãra ya ce bai sani ba. Tãwĩlin Alƙur'ãni ko Hadĩsi da hankali yana kai ga bũɗe ƙõfar kãfirci ɓõyayye da yin hukunci da abin da Allah bai saukar ba. Na'am ba a hana ijtihãdi ga abin da ba a sãmi nassi a kansa ba, ko kuma aka sãmi nassi wanda bã bayyananne ba. Jingina ijtihãdi ga ra'ayi ya fi tãwĩlin abin da bai bayyana ba daga Alƙur'ãni ko Hadĩsi, domin ra'ayi ba ya ɓatar da wasu, amma tãwĩli yana ɓatarwa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net