An-Nisaa 4:114
النساءلَّا خَيْرَ فِى كَثِيرٍ مِّن نَّجْوَىٰهُمْ إِلَّا مَنْ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوْ مَعْرُوفٍ أَوْ إِصْلَـٰحٍۭ بَيْنَ ٱلنَّاسِ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ ٱبْتِغَآءَ مَرْضَاتِ ٱللَّهِ فَسَوْفَ نُؤْتِيهِ أَجْرًا عَظِيمًا
Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu[1] fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.
[1] Hukuncin gãnawa da Annabi ko wani shũgaban jama'a mai tsayuwa matsayin Annabi ga gyãran sha'aninsu, bã ya halatta sai idan akwai wani alheri a ciki wanda amfaninsa zai shãfi jama'a duka.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net