Aal-i-Imraan 3:75
آل عمرانوَمِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ مَنْ إِن تَأْمَنْهُ بِقِنطَارٍ يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيْكَ وَمِنْهُم مَّنْ إِن تَأْمَنْهُ بِدِينَارٍ لَّا يُؤَدِّهِۦٓ إِلَيْكَ إِلَّا مَا دُمْتَ عَلَيْهِ قَآئِمًا ۗ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا۟ لَيْسَ عَلَيْنَا فِى ٱلْأُمِّيِّـۧنَ سَبِيلٌ وَيَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ وَهُمْ يَعْلَمُونَ
Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri,[1] zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai.[2]" Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.
[1] Ƙinɗar Shi ne ũƙiyya dubũ gõma sha biyu, kuma ũƙiyya ɗaya tanã daidai da dirhami dubũ biyu da ɗari biyar kõ dĩnari dubu.
[2] Bãbu laifi idan mun ci dũkiyarsu: Watau Bayahũde yana ganin cin dũkiyar wanda bã Bayahũde ba irinsa halal ne a gare shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net