Aal-i-Imraan 3:36
آل عمرانفَلَمَّا وَضَعَتْهَا قَالَتْ رَبِّ إِنِّى وَضَعْتُهَآ أُنثَىٰ وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا وَضَعَتْ وَلَيْسَ ٱلذَّكَرُ كَٱلْأُنثَىٰ ۖ وَإِنِّى سَمَّيْتُهَا مَرْيَمَ وَإِنِّىٓ أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ ٱلرَّجِيمِ
To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu[1] kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe."
[1] Maryam, ma'anarta mai ibãda. Abinci da ake kai mata a cikin Masallaci shĩ ne 'ya'yan itãce, irin na ɗãri, a lõkacin bazara, kuma irin na bazara a lõkacin ɗãri. Wannan kuma ya mõtsar da begen zakariyya ga sãmun ɗã, bãyan shi da mãtarsa sun tsũfa ba su haifu ba. Sai ya rõƙi Allah kuma Ya karɓa masa, Ya ba shi Yahaya Annabi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net