Aal-i-Imraan 3:35
آل عمرانإِذْ قَالَتِ ٱمْرَأَتُ عِمْرَٰنَ رَبِّ إِنِّى نَذَرْتُ لَكَ مَا فِى بَطْنِى مُحَرَّرًا فَتَقَبَّلْ مِنِّىٓ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
A lõkacin da mãtar Imrãna[1] ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani."
[1] Mãtar Imrãna sunanta Hannatu ɗiyar fãƙũza, bã ta haifuwa, sai wata rãna ta ga tsuntsuwa tanã ciyar da tsãkonta, sai ta yi sha'awar sãmun ɗa sabõda haka ta rõki Allah Ya bã ta ɗa. Da mijinta Imrãna ya tãke ta sai ta sãmi ciki, dõmin murna sai ta yi alkwarin 'yanta shi da bakance ga Masallacin Baitil Muƙaddas dõmin ya riƙa yi masa hidima. To, a lõkacin da ta haihu sai ta sãmi ɗiya mace. Ga shari'arsu bã a 'yanta mace ga irin wannan aiki na hidimar masallaci, dõmin haka ta nemi uzuri da cewa ta haife ta mace, mace bã kamar namiji take ba. Har ta yi ruɗu ta jũya, ta ce, namijin bã kamar mace ba, dõmin namiji ne a cikin zũciyarta.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net