Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 28 · Aya ta 81

Al-Qasas 28:81

القصص

فَخَسَفْنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلْأَرْضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٍ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلْمُنتَصِرِينَ

Ma’ana

Sai Muka shãfe ƙasa[1] da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.

[1] An ce a bãyan Ƙãrũna ya yanke kansa da nasa mutãne daga Mũsã, sai ya shirya da wata kãruwa dõmin ta yi wa Mũsã ƙazafin cewa ya yi zina da ita, a kan ya aure ta. Sai Mũsãya tãshi yanã wa'azi a cikin Banĩ Isrã'ĩla ya ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla wanda ya yi sãta zã mu yanke hannunsa, wanda yayi ƙazafi mu yi masa bũlãla tamãnin, wanda ya yi zina, bã ya da mãtã, mu yi masa bũlãla ɗãri, wanda ya yi zina yanã da mãtã, mu jefe Shi sai yã mutu." Sai Ƙãruna ya ce: "Kõ dã kai ne?" Ya ce: "Kõ da ni ne." Sai Kãrũna ya ce: "An ce kã yi fãjirci tãre da wance, kãruwa." Sai Mũsã ya ce: "A kirã ta" Da ta zo, ya gama ta da Allah, ta faɗi gaskiya, sai ta ce Ƙãrũna ne ya yi tsãda da ita, ta faɗi hakanan. Sai Mũsã ya yi addu'a a kansa, ƙasa ta haɗiye shi, shi da gidansa duka.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Qasas

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net