Al-Qasas 28:80
القصصوَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ وَيْلَكُمْ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيْرٌ لِّمَنْ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai,[1] kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai haƙuri."
[1] ĩmãni da aikin ƙwarai wanda Allah Ya yi umurni da a yi shi, kuma yinsa kamar yadda ManzonSa ya nũna. Akwai daga cikin aikin ƙwarai yin hijira da barin kula da dũkiya. Bã a sãmun sakamakon Allah sai da haƙuri.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net