Al-Hajj 22:52
الحجوَمَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ وَلَا نَبِىٍّ إِلَّآ إِذَا تَمَنَّىٰٓ أَلْقَى ٱلشَّيْطَـٰنُ فِىٓ أُمْنِيَّتِهِۦ فَيَنسَخُ ٱللَّهُ مَا يُلْقِى ٱلشَّيْطَـٰنُ ثُمَّ يُحْكِمُ ٱللَّهُ ءَايَـٰتِهِۦ ۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ
Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri,[1] sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyin Sa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
[1] Annabãwa sukan yi wahami ga tunãninsu, su yi zaton wani abu daidai ne alhãli kuwa a wurin Allah bã haka Yake nufi ba. A kan wannan, sai shakka ta shiga wãwã a kansu, amma wanda ke da ĩmãni to bã zai rikice ba sabõda wannan kuskure dõmin Allah bã Ya barin su a kansa, sai Ya gyãra abin da ke ciki na wahami. Misãli ƙissar Yũnusu, da ƙissar Annabi a cikin suratu Abasa, da ƙissar Ibrãhim wajen jãyayya da malã'ikun da aka aika zuwa alƙaryõyin mutãnen Lũɗu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net