Al-Anbiyaa 21:80
الأنبياءوَعَلَّمْنَـٰهُ صَنْعَةَ لَبُوسٍ لَّكُمْ لِتُحْصِنَكُم مِّنۢ بَأْسِكُمْ ۖ فَهَلْ أَنتُمْ شَـٰكِرُونَ
Kuma Muka sanar da shi sana'ar[1] wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?
[1] Wannan yanã nũna wajabcin yin sana'a wadda mutum ke rãyuwa a kanta. Kuma yanã nũna wajabcin aiki da sabubba dõmin neman tsaron kai. Bã ya halatta ga mutum ya yi kwance bãbu sanã'ar da zai tsayu a kanta Kõ kuma ya gĩtta kansa ga halaka da tãwilin tawakkali. Tawakkali shĩ ne mayar da ãƙibar al'amura ga Allah a bãyan mutum ya yi abinda yake iya yi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net