Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 21 · Aya ta 79

Al-Anbiyaa 21:79

الأنبياء

فَفَهَّمْنَـٰهَا سُلَيْمَـٰنَ ۚ وَكُلًّا ءَاتَيْنَا حُكْمًا وَعِلْمًا ۚ وَسَخَّرْنَا مَعَ دَاوُۥدَ ٱلْجِبَالَ يُسَبِّحْنَ وَٱلطَّيْرَ ۚ وَكُنَّا فَـٰعِلِينَ

Ma’ana

Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar)[1] ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.

[1] Asalin mats'alar, tumãkin wani mutum suka yi kĩwon ɓarna a gõnar wani a cikin dare alhãli kuwa anã kallafa wa mai dabbõbi ya kange dabbõbinsa da dare kamar yadda ake kallafa wa mai shũka da tsare shũkarsa a cikin yini. Sai Dãwũdu ya yi hukunci da cewa mai shũkar ya mallaki tumakin, shi kuma mai tumãki ya mallaki shũkar ɓãtacciya. Sai Sulaimãn ya gyãra hukuncin da cħwa mai gõna ya riƙi tumãkin ya rãyu a kansu har a lõkacin da mai dabbõbin ya gyãra masa gonarsa har ta Koma yadda take a farKon lõkacin,sa'an nan ya mayar da tumãkin ya karɓi gõnarsa. A cikin ƙissar akwai nũnin cewa Annabãwa bã su saunar faɗin gaskiya, sabõda wani mutum duk yadda yake, kuma anã warware hukunci idan kuskure ya auku a ciki, kuma Annabãwa sunã yin kuskure ga abin da bai shãfi wahayiba. Kuma kõmãwa ga askiya idan tã bayyana wajibi ne.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Anbiyaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net