Al-Baqara 2:273
البقرةلِلْفُقَرَآءِ ٱلَّذِينَ أُحْصِرُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا يَسْتَطِيعُونَ ضَرْبًا فِى ٱلْأَرْضِ يَحْسَبُهُمُ ٱلْجَاهِلُ أَغْنِيَآءَ مِنَ ٱلتَّعَفُّفِ تَعْرِفُهُم بِسِيمَـٰهُمْ لَا يَسْـَٔلُونَ ٱلنَّاسَ إِلْحَافًا ۗ وَمَا تُنفِقُوا۟ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ
(Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan[1] nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.
[1] Matalautan nan 'muhãjiruna'ne waɗanda suka bar dũkiyarsu da iyãlansu dõmin hijira. Kuma ba su sãmi wata matãka ba a Madĩna, sai aka yi musu rumfuna, sunã kwãna a ciki, suka tsare kansu dõmin jihãdi da yãƙi da karãtun Alƙur'ãni da ibãda kamar matsayin sõja a yanzu. Sũ wajen ɗari huɗu ne, shugabansu, shi ne Abdur Rahman bn Sakhar Abu Huraira el Dawsy.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net