Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 223

Al-Baqara 2:223

البقرة

نِسَآؤُكُمْ حَرْثٌ لَّكُمْ فَأْتُوا۟ حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا۟ لِأَنفُسِكُمْ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّكُم مُّلَـٰقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Ma’ana

Mãtanku gõnaki ne a gare ku,[1] sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.

[1] Mutum na iya sãduwa da mãtarsa yadda yake so kuma yadda ya sauƙaƙa a gare shi, daga gaba kõ daga bãya, amma ga farji banda ga dubura. Ma'anar ku gabãtar da alheri dõmin rãyukanku, shi ne ku yi basmala ku nemi tsari daga Shaiɗan sabõda 'ya'yanku. Ba a jimã'i da mace alhãli tanã barci, ana son gabãtarda wãsa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net