Al-Baqara 2:197
البقرةٱلْحَجُّ أَشْهُرٌ مَّعْلُومَـٰتٌ ۚ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ ٱلْحَجَّ فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِى ٱلْحَجِّ ۗ وَمَا تَفْعَلُوا۟ مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ ٱللَّهُ ۗ وَتَزَوَّدُوا۟ فَإِنَّ خَيْرَ ٱلزَّادِ ٱلتَّقْوَىٰ ۚ وَٱتَّقُونِ يَـٰٓأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ
Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji[1] a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula.
[1] Bayãnin abũbuwan da aka hana a cikin hajji da waɗanda ake son a yi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net