Al-Baqara 2:104
البقرةيَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَقُولُوا۟ رَٰعِنَا وَقُولُوا۟ ٱنظُرْنَا وَٱسْمَعُوا۟ ۗ وَلِلْكَـٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã'[1] kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi.
[1] 'Rã'ina,' magana ce mai ma'ana iri biyu ta yabo da ta zãgi. Ta farko ita ce a lõkacin; da Annabi ke karantar da Sahabbansa sai su ce, 'ra'inã' watau dãkata mana har mu gane wannan; ta biyu ita ce, ra'inã!, watau yã ruɓaɓɓe! To, idan Sahabbai sun ce, 'ra'ina,' sunã nufin ma'anar farko, sai Yahũdu da mushirikai su jũya musu magana da ma'ana ta biyu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net