Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 19 · Aya ta 64

Maryam 19:64

مريم

وَمَا نَتَنَزَّلُ إِلَّا بِأَمْرِ رَبِّكَ ۖ لَهُۥ مَا بَيْنَ أَيْدِينَا وَمَا خَلْفَنَا وَمَا بَيْنَ ذَٰلِكَ ۚ وَمَا كَانَ رَبُّكَ نَسِيًّا

Ma’ana

(Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka[1] Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma[2] (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.

[1] 'Yan Aljanna sunã cewa ba mu sauka a waɗannan gidãje ba sai da umurnin Ubangijinka, kai mai karatu, A1lahne Mai mallakar kõme, kuma kõme ãyã ne mai nũni zuwa gare shi, sabõda haka bã a mantãwa da shi.
[2] Maganar Allah ce a bãyan maganar 'yan Aljanna dõmin ta'aƙĩbi da ƙãrin bayãni ga maganarsu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Maryam

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net