Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 19 · Aya ta 59

Maryam 19:59

مريم

فَخَلَفَ مِنۢ بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّبَعُوا۟ ٱلشَّهَوَٰتِ ۖ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا

Ma’ana

Sai waɗansu 'yan bãya[1] suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.

[1] An ruwaito cewa wannan zai auku a lõkacin Tãshin Ƙiyãma ne a bãyan tafiyar sãlihan wannan al'umma ta Muhammadu. Zã su dinga barbarar jũnansu a cikin hanyõyi. Su tõzarta salla, su gina manyan gidãje su hau dukan abin da aka hana su, su tufanci abin da aka hana su, Ƙurɗabi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Maryam

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net