Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 28

Al-Kahf 18:28

الكهف

وَٱصْبِرْ نَفْسَكَ مَعَ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ رَبَّهُم بِٱلْغَدَوٰةِ وَٱلْعَشِىِّ يُرِيدُونَ وَجْهَهُۥ ۖ وَلَا تَعْدُ عَيْنَاكَ عَنْهُمْ تُرِيدُ زِينَةَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ وَلَا تُطِعْ مَنْ أَغْفَلْنَا قَلْبَهُۥ عَن ذِكْرِنَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ وَكَانَ أَمْرُهُۥ فُرُطًا

Ma’ana

Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardar Sa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya.[1] Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncin Mu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna.

[1] Ãyõyi na ashirin da bakwai da ashirin da takwas sunã umurni da bin shari'a ta Alƙur'ãni, kuma sunã hani daga bin son zũciya dõmin nħman ƙawar rãyuwar dũniya wadda aka yi dõmin a jarrabi wãwã da ita, sa'an nan ta kõma turɓãya ƙeƙasasshiya. Dũbi ãya kuma, ta takwas da ta tara. Mun dai sani, cewa umurni da bin sharĩ'a bayyananna shĩ ne kan labarin sũrar.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net