Al-Kahf 18:110
الكهفقُلْ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يُوحَىٰٓ إِلَىَّ أَنَّمَآ إِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۖ فَمَن كَانَ يَرْجُوا۟ لِقَآءَ رَبِّهِۦ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَـٰلِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦٓ أَحَدًۢا
Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa."[1]
[1] Wannan ãya, a dunƙule, ta tãra dukan abin da ke cikin sũrar. Allah Ya shiryar da mu, ga kaɗaita shi ga ibãda, da yin ibadar, kuma yadda Allah Ya ce a yĩ ta, ga mai tsammãnin rabo a Lãhira. Wanda ba ya tsammãnin rabon Lãhira, ya tsaya ga dũniya mai gushħwa da sauri, to, shĩ bã a shiga batunsa ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net