Al-Kahf 18:109
الكهفقُل لَّوْ كَانَ ٱلْبَحْرُ مِدَادًا لِّكَلِمَـٰتِ رَبِّى لَنَفِدَ ٱلْبَحْرُ قَبْلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَـٰتُ رَبِّى وَلَوْ جِئْنَا بِمِثْلِهِۦ مَدَدًا
Ka ce: "Dã tẽku[1] ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."
[1] Ma'anar ãyar nan ita ce Allah ne Mafi sani. llmin Allah bã shi da iyãka, kõ kalmõmin da suka ɗauki ma'anõninsa, bã zã a iya rubuta su ba, balle ma'anõnin da ke cikinsu. Sabõda haka abin da ke hankali a mutum, shĩ ne ya yi aiki da ɗan ilmin da Allah Ya umurce shi da aiki dashi. Idan ya nemi ya wuce nan, to, ya halakar da kansa dõmin bai san inda zai fãɗa ba. Wannan ilmin shi ne sharĩ'a da aiki da ita.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net