Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 16 · Aya ta 68

An-Nahl 16:68

النحل

وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى ٱلنَّحْلِ أَنِ ٱتَّخِذِى مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا وَمِنَ ٱلشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ

Ma’ana

Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi[1] zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa."

[1] Wahayi na ilhama, watau Allah Ya cũsa wa ƙudan zama ilmin yin sã ƙar gidan zuma da gãne hanyõyin tafiya ta kõma gidanta, da cin kõwane irin furen itãce dõmin a fitar dani'imar abin sha mai dãdi ga mutãne, kuma wanda ya ƙunsa dukkan mãgani ga ciwarwatansu. Wannan ni'ima ce babba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nahl

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net