Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 16 · Aya ta 67

An-Nahl 16:67

النحل

وَمِن ثَمَرَٰتِ ٱلنَّخِيلِ وَٱلْأَعْنَـٰبِ تَتَّخِذُونَ مِنْهُ سَكَرًا وَرِزْقًا حَسَنًا ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ

Ma’ana

Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye[1] da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.

[1] Yã ambaci abin mãye a cikin abũbuwan ni'ima a gabãnin aharamta giya. Kuma haramtã ta bã ya hanã ta zuma a cikin ni'imõmin Allah ga mutãne dõmin an haramtã ne sabõda tsaron hankalinmu a kan neman waɗansu ni'imõmin da suka fĩ ta a Aljanna a inda bã zã a hana ta ba sabõda ƙarewar taklĩfi a can. Sabõda haka ne ya ƙãre ãyar da cewa: "Akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta.".

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nahl

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net