Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 13 · Aya ta 14

Ar-Ra'd 13:14

الرعد

لَهُۥ دَعْوَةُ ٱلْحَقِّ ۖ وَٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسْتَجِيبُونَ لَهُم بِشَىْءٍ إِلَّا كَبَـٰسِطِ كَفَّيْهِ إِلَى ٱلْمَآءِ لِيَبْلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَـٰلِغِهِۦ ۚ وَمَا دُعَآءُ ٱلْكَـٰفِرِينَ إِلَّا فِى ضَلَـٰلٍ

Ma’ana

Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama[1] ba fãce yanã a cikin ɓata.

[1] Allah Mamallakin ruwa, Yanã kiran mutãne dõmin Ya bã su ruwan su shã. Su kuma kãfirai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam waɗanda kõ karɓa musu kiran bã zã su iya yi ba, kuma sunã neman ruwa daga gare su, alhãli kuma ba su mallaki kõme ba. Watau Mai abu Yanã kiran su dõmin Ya bã su, sun ƙi karɓa Masa sai sunã kiran wani wanda bai mallaki kõme ba, sunã rõƙon Sa ruwa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Ar-Ra'd

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net