Yusuf 12:8
يوسفإِذْ قَالُوا۟ لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَىٰٓ أَبِينَا مِنَّا وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ
A lõkacin da suka ce:[1] lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.
[1] Hĩrar yãra a tsakãninsu. Sunã tunãnin sõyayyar ubansu ga ɗayansu wanda bã ya cikinsu yanzu. Sunã tunãnin yadda zã su sãmi ãdalcin daidaitãwar so daga ubansu bãki ɗayansu. Ɗan'uwansu wanda ubansu yake so, watau Yũsufu, ya sãmi baƙin jini daga gare su dõmin ubansu yana sonsa. Sabõda haka shaiɗan yanã sanya musu tunãnin su yi zunubin rabuwa da shi, sa'an nan su tũba ga Allah.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net