Yusuf 12:7
يوسفلَّقَدْ كَانَ فِى يُوسُفَ وَإِخْوَتِهِۦٓ ءَايَـٰتٌ لِّلسَّآئِلِينَ
Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi[1] sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa[2] dõmin mãsu tambaya.
[1] Ãyõyi a nan, anã nufin hãlãye waɗanda suka zama darussa na kõyarwa ga mutãne dõmin tarbiyya ga yãra da manya na kõwane matsayi ga rãyuwar ɗan Ãdam.
[2] Yũsufu da ɗan'uwansa shaƙĩƙi, Binyãmĩnu, da sauran gõma. Babbansu ga shekaru, shi ne Raubĩlu, kuma sai Lãwiya. A cikin gidansa aka yi Annabãwa, sai Yahũza kuma shĩ ne shũgabansu a ra'ayi, shĩ ne uban sarãkunansu, sabõda haka sũnansa ya rinjãya a kan ƙabĩlar, aka ce musu Yahũdu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net