Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 12 · Aya ta 67

Yusuf 12:67

يوسف

وَقَالَ يَـٰبَنِىَّ لَا تَدْخُلُوا۟ مِنۢ بَابٍ وَٰحِدٍ وَٱدْخُلُوا۟ مِنْ أَبْوَٰبٍ مُّتَفَرِّقَةٍ ۖ وَمَآ أُغْنِى عَنكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَىْءٍ ۖ إِنِ ٱلْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ ۖ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ ۖ وَعَلَيْهِ فَلْيَتَوَكَّلِ ٱلْمُتَوَكِّلُونَ

Ma’ana

Kuma ya ce: "Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam,[1] kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara."

[1] Yãƙũbu ya umurci ɗiyansa su shiga garin, ta ƙõfõfi dabam- dabam, yanã nũna cewa yanã gudun kyawunsu da yawansu zai ja hankalin mutãne zuwa gare su. A cikin mutãne akwai mãsu kambun baka da mugun nufi kõ da yake Yãƙũba a cikin hãlin haka ya aza tawakkalinsa ga Allah. Ya yi abin da yake zaton alhħri ne, wanda bai saɓa wa sharĩ'a ba. Amma kuma yã yi haka ne a kan wani ilmi da Allah Ya sanar da shi cewa a wannan fitar tãsu ce Allah zai yi sanadin sãke sãduwarsu da Yũsufu, sabõda haka ya umurce su da su shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, dõmin mutum shi kaɗai yã fi sãmun dãmar ta'ammalin ganin mutãne da abũbuwa. Kuma ta yin haka, yanã tsammãnin waninsu zai ga Yũsufu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Yusuf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net